Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan kusan Wata biyu a ƙasar london.
Buhari ya dawo bayan kwana 49 da ya bar Najeriya zuwar London domin duba lafiyar sa. Saboda filin jirgin Abuja a rufe yake, Jirgin samansa ta sauka a kaduna.
Jirgin Air force 001 na Najeriya ne ya dauka shugaba suka sauka a filin jirgi a Kaduna. Bayan sun iso, sai aka ɗauko shi a cikin helikofta aka kai shi gidan Shugaba a Abuja.
Akwai rahotani wai ƙila Buhari ya magance al'umma a yau bayan hutun sa, domin ya kwantar da wasu damuwa game da mulkin sa.
Kakakin Buhari akan kafofin watsa labarai Femi Adesina, shi ya watsa labarin dawowar sa da dare ranar alhamis, 9 na watan Maris, 2017.
Buhari ya bar Najeriya, na hutun kwana 10, ya ce a wannan lokacin zai je binciken lafiyar sa. Anjima dai sai aka miƙanta hutun, saboda shawarar likitoci da suka ce za su kara wasu gwaje-gwaje..
from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online http://ift.tt/2mw8FJD
via IFTTT
