Ojodu ya ce babu abin da aka yi tun lokacin da Osibanjo ya hau mulki, da Buhari bai riga shi farawa ba.
Babafemi Ojodu, kakakin Muhammadu Buhari a kan siyasa, ya lalata yabon da ake yi wa Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osibanjo akan aikin da ya ke yi.
Yan nijeriya sun ci gaba da yabon Osibanjo tun lokacin da Buhari yayi tafiya zuwa ƙasar London wurin binciken lafiyar sa, wasu sun ce ya fi shugaban ƙasa aiki mai kyau.
Amma Ojodu ya ce Osibanjo aikata Tsarin da aka jera kawai ya ke yi.
A lokacin da ya ke magana da ƴan jarida a ranar litinin , 27 Febwairu, ya bayyana cewa duk abubuwan da Osibanjo ke yi, Buhari ya riga shi farawa, ya zargi ƴan “Peoples Democratic Power” (PDP), da niyar jawo rabuwa tsakanin su, da cewa mutum guda ya fi guda.
Ya ce “Babu abun da aka yi da ba a riga aka fara ba a ƙarkashin shugaba”
“A tunani na, bai dace ba, sannan a gani na, niyar ƴan hammaya ne kawo rabuwa.
“Haka mutanen da suka ce ba mu da tawagar tattalin arziki, ba tsari, su suka ce wannan. A yanzu tsarin da muke aikatawa na girma kuma suna ganin sakamakon ... ba tambayar wanda ya fi wani bane.
“Zan baku misali, babu abin da aka yi tun lokacin da mataimakin shugaba ya fara aiki da ba a riga aka fara tun lokacin baya ba, misali mai kyau shi ne tsare tsaren Niger Delta, Shugaban ƙasa ya kira mataimakin sa, ya ce, na ba ka iko, ka je Niger Delta tare da kowa da kowa, da al’ummar su, ku rike magana da tsagera domin shirya waɗannan matsalolin domin amfanin ƴan nijeriya, wannan shawarar na shugaban ƙasa ne, ba na mataimakin sa ba.
“Ina faɗa muku cewa, ni na gan cewa ana biɗar jawo rabuwa, kuma da gan gan.
“Wasu mutane sun kushe kowa a lokutan baya, ina ganin su a twitter da facebook, ko ina a kafofin watsa labarai, suna ƙoƙarin jawo rabuwa tsakanin mu, kuma mu ba za mu yarda da wannan ba, Shugaba da mataimakin sa su na aiki mai kyau tare, kuma na san suna da Aminci guda game da wannan ƙasar.
Da aka tambaye shi ko Osibanjo na neman shawarar Shugaba Buhari, Ojodu ya ce “a kowace rana, saboda akwai wuraren da dole sai ya biɗa shawarar shugaba, ba
Ko da yaushe ba, amman akwai yanka shawarar da dole sai ya nemi shawara a wurin shugaba, Shugaba har yanzu shi ne shugaban Najeriya.
Ya fi masaniya, kuma ya daɗe a siyasa fiye da mataimakin sa, in akwai yankan shawara mai muhimmanci da ya kamata ya dauƙa, dole ya kira shi ya nemi shawarar shi ya ce “yallaɓai menene tunanin ka game da wannan shawarar da muke son mu yanka, menene ra’ayin ka?” bai nufin ba ya da iko.”
A yanzu, ba a san lokacin da Buhari zai dawo daga kasar London ba, saboda ya na buƙatar dogon lokaci domin hutawa.
from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online http://ift.tt/2lRPytw
via IFTTT
