Review Cart.


Checkout Summary.

Total
Items:
> Total
Amount:
+ Delivery:+ Tax:= GRAND
TOTAL:

Send Order Pay with Paypal
View Cart () items.

Friday, 17 March 2017

A Abuja: Yara 4 sun nitse a Kogin Galadimawa a Abuja, FCT


Yara 4 sun nitse a Kogin Galadimawa a Abuja, FCT

Rahotan NAN ya ce, mutane 4 tare da wasu yara suna wanki a bakin kogin a lokacin da hatsarin ya faru.

Yara huɗu, Jinkai Hakila, 10, Bridget Ibrahim, 11, Precious Ezra, 14  da Azumi Daniel, 16 sun nitse a kogin Danko, a Al’ummar Galadimawa, a FCT, Abuja.

Waƙili daga NAN da ya je ziyara a al’umman ya ba da rahota cewa Mazaunin garin suna jimamin mutuwar yaran, bayan hatsarin.

NAN sun ba da rahota cewa ƴaƴan da suka rasu suna tare da wasu yara a bakin kogin a lokacin da hatsarin ya faru.

Wasu masu shaida sun faɗa wa NAN cewa hatsarin ya faru a lokaci 11 na safe, a lokacin yaran suna wanki a bakin kogin.

Blessing Elisha, mai shekara 14, ta gaya wa NAN Cewa gaba ɗayan su na tare suna wanki, kuma wasu yaran na wasa a lokacin da hatsarin ya faru.

Ta ce himman hana su wasa kusa da kogin bai yi aiki ba.

Ban gani lokacin da suka shiga ruwan ba, saboda ina wanki, kwatsam kawai sai aka kira ni, cewa su uku sun shiga cikin Kogin.”

Da na kalla sama sai na ga shigan na hudun, na yi ƙoƙarin ƙubutar da ita, amma sai na ga kamar ina nitsawa.

Sai na ƙyale ta, na gudo kiran taimako.” ta ce.

Alhassan Abdulwahab, wani cikin mutane na farko da suka amsa kiran ƙuncin, ya ce ya kai hour 3 kafin aka fitar da gawan su daga kogin.

Ya ce bayanan da aka samu daga sauran yaran a gurin ya nuna cewa mai ƙanƙantar shekaru a cikin su, Hakila itace ta farko da ta shiga kogin.

Ya ce sauran yaran sun nitse in da suke yunƙurin ƙubutar da abokan su.

Mun iso gurin nan take da jin bayani, ya dauƙi yan lokuta kafin muka gano gawayen su, saboda ragan mu na kamo kifi na cikin kogin.

Bayan na jawo ragan da babbar kifi a ciki, na gano gawa guda huɗu a gurin, cikin su bai kumbura ba, Abdulwahab ya ce.

NAN sun bada da rahota cewa an burne gawan yarda Al’adar su ta ce.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online http://ift.tt/2nvx5rZ
via IFTTT

Mix Theme

Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. Praesent id purus risus. Nulla sit amet velit eleifend, porta diam vehicula, cursus urna.
Your Picture

about me

about me

favourite Posts