Ƙungiyar Sapphire Foundation sun rarraba ma mutane masu tafiya da tsiraicinsu kayan taimako.
Mun kawo muku hotunan Birnin Amina a Jihar Niger, gari wanda mutane suna tafiya da tsiraicinsu domin rashin sutura.
Maʼaikatan ƙungiyan sun kai ziyara zuwa Ƙaramar Hukuma na Rijau a Jihar Niger domin taimaka wa mutanen garin da sutura.
Yara, Manya, Mata da Mazaje, suna tafiya da tsiraici a wannan gari. Ƴan Ƙungiyar Sapphire Foundation sun kawo musu farin-ciki a yayin da sun kawo ma mutanen ƙauyen kayayyaki. Haka kuma mutanen sun ƙarbe su da farin-ciki.
Ana shawarwari da kuma shirin gina musu Makaranta. Menene ya hana Gwamnati, ƙungiyoyin addini da ƴan siyasa su ɗauki irin wannan mataki?
from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online http://ift.tt/2lo9AA3
via IFTTT
